KO KUWA KA SAN DALILIN SANYAWA RAKE (SUGAR CANE) JAR KANWA {POTASSIUM CARBONATE}

 KO KUWA KA SAN DALILIN SANYAWA RAKE (SUGAR CANE) JAR KANWA  {POTASSIUM CARBONATE}


Fitar Ranar: Litinin 4th December, 2023


Abin Cikin Rubutu:-

1. Me ne ne Rake?

2. Me ce ce Jar kanwa.

3. Muhimmancin Rake ga lafiya.

4. Amfanin Jar kanwa a Rake ta Fuskar Lafiya da Kasuwa.

____________________________________________________

ME NE NE RAKE?

Rake dai shuka ce mai dogon zango (perennial plant), mai tsayi kimanin kafa 10 zuwa 15 (10-15 feet) haɗi da gaɓoɓi a jikin sa, mai siraran ganye, Launin Shuɗi mai duhu ko Kore mai haske ta waje sannan farin launi a ta ciki, Sananne wajen samun Sukari (Sugar).


ME CE CE JAR KANWA?

Jar kanwa na cikin sinadarai  na ma'adanan kasa (Minerals) wato  Potassium carbonate/Crude potash/Potash lye da harshe Turanci, yanayinta kamar Ƙasa ko Marmara, sannan tana iya narkewa a cikin ruwa. Ana amfani da ita wajen samar da sinadarin Taki (Fertilizer), yin Sabulu harma da haÉ—a Glass. Dss


MUHIMMANCIN RAKE GA LAFIYA


Rake yana da matuƙar Muhimmancin ga lafiya wanda tun zamanin Da mutane da yawa sukanyi amfani da shi da fuskokin mabanbanta, wanda a wannan zamanin namu bincike ya kara tabbatar da Muhimmancin sa da kuma amfanin sa ga lafiya, kamar haka:


1. Karfafa Kuzari (Energy Booster):  Sinadarin Carbohydrate da Rake ke É—auke da shi yana da saurin dawo da kuzari a cikin jiki, da kuma taimakawa jiki wajen yin aiki yadda ya kamata.


2. Taimakawa wajen Narkar da abinci:  Ruwan Raken na taimakawa wajen rura halittun dake narka abinci a cikin ciki.


3. Taimakawa lafiyar Hanta (Liver):  Ruwan Raken na É—auke da MahaÉ—ina "HEPATOPROTECTIVE" wanke shi wannan na kare Hanta daga barin Lalacewa.


4. Dai-daita yanayin jiki:  Ruwan Rake hanya ce ta ainihi wajen samun muhaÉ—in "ELECTROLYTES" kamar: Sinadarin Potassium da Sinadarin Magnesium, wanda yana taimakawa wajen sassaita ruwan jiki, dai-daita gudanar jini, taimakawa tsokar jiki da taimakawa aikin jijiyoyin jini.


5. Kasancewar Sinadarai masu ... (Antioxidant properties): Ruwan Rake na É—auke da Sinadarin Vitamin C da Flavonoids, waÉ—annan sinadarai su na kare Æ™wayar halitta (cell) daga barin Lalacewa. WaÉ—annan Antioxidant din taimakawa wajen rage kumburin jiki da  Æ™aranta barazanar tsanantar cuta. Dss


AMFANIN JAR KANWA A RAKE TA FUSKAR LAFIYA DA KASUWA

Anan kasar Hausa musamman cikin garin Kano masu sana'ar siyar da Rake musamman masu gutsura shi kanana su na amfani da Jar kanwa bayan sun jiƙata acikin ruwa, sai su ringa fesawa Raken ruwan jar kanwar da nufin rage Ƙuda (Tsetse Fly) da kuma yin aiki a matsayin Sinadari mai bada launi (colouring agent).

Yayin da ka fesawa Rake ruwan jar kanwar yana sawya launi daga Farin launi zuwa launin Rawaya mai haske (Kalar Madara). 


Muhimmancin sanya Jar Ƙanwar ga Kasuwa:

1. Raken da aka sanya masa jar kanwa yana zamowa mai É—aukar hakali fiye da wanda ba'a sanya masa ba sabo da ruwan na taimakawa danshi jikin Rake.

2. Yana taimakawa wajen Rage Ƙudaje wanda hake ke bada gudunmawa wajen tsaftar Raken da kiyaye shi ga gurɓata. Dss


Muhimmancin sanya Jar Ƙanwar ga Lafiya:

1. Taimakawa wajen rage zaƙin Raken musamman ga mutanen dake fama da cutar ciwon Suga (Diabetes).

2. Tana taimakawa wajen rage gurɓa tar sa wanda sakamakon gurɓatar ka iya haifar da matsala ga lafiya. Dss





Daga karshe, yana da muhimmanci ga mutanen dake fama da cutar ciwon Suga (Deabites) dasu shawarci likitan su kafin su yi amfani Raken ta fuskar lafiya, matsatstsen ruwan Raken ne (juice) ko kuma taunawa za'ayi. Hakazalika babu idan an sanyawa Raken ruwan jar kanwar ta ɓarin inda aka yanka shi da yuhuwar ya dan rage zaƙin sa, amma su masu siyarwa idan kazo siya dasun yake gafennin nasa sai zaƙin nasa ya kara fitowa.

__________________________________________________

Naku: Hussaini Sani Sodangi

B.Tech (Hon) Food Science and Technology (Inview), ADUSTECH.

+2348147146681

hussainissodangi@gmail.com


Saudaukarwa zuwa ga:

Auwal Musa Ibrahim

Mai bada shawara kan harkokin Shari'a na kamfanin

El-husaso Global Limitedd

Post a Comment

0 Comments